Rundunar sojin saman Nijeriya, ta tura jragen yaki zuwa wuraren da za a iya samun Baraka domin su taimaka wa sauran hukumomin tsaro wajen tabbatar da zaman lafiya a lokacin zabe.
Kakakin rundunar Air Commodore Ibikunle Daramola ya bayyana haka, yayin wani taron manema labarai da ya gudana a Abuja.
Daramola ya ce, Shugaban rundunar sojin sama Air Marshal Sadique Abubakar ya bayyana hakan, yayin wani taron manyan ma’aikatan rudunar da kwamandoji a helkwatar ta da ke Abuja.
Kakakin rundunar ya ce an yanke shawarar ne daidai da umurnin Shugaban ma’aikatan tsaro Janar Abayomi Olonisakin, wanda ya umurci hukumomin tsaro su tabbatar an gudanar da zaben gwamnoni da na majalisun jihohi cikin lumana.
A cewar sa, an yi shirin ne ko da za a samu matsalar karya doka da oda.