Muhammadu Buhari, Shugaba Kasa
Muhammadu Buhari, Shugaba Kasa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya bukaci ‘yan Nijeriya su fito kwan su da kwarkwatar su domin kada kuri’a a zaben gwamnonin da na ‘yan majalisun jihohi da zai gudana a wannan makon.

Buhari ya kuma bukaci masu kada kuri’a su kwamnar da hankulan su, tare da bin dokokin da hukumomi su ka shimfida a lokacin gudanar da zabubbukan.

Ya ce akwai hukunce-hukunce masu tsanani da za a dauka a kan wadanda aka samu da laifuffukan da su ka shafi satar akwati, da magudin zabe, da tada hatsaniya da sauran su.

Shugaba Buhari, ya ce jami’an tsaro za su cigaba da aikin tsaron lafiya da dukiyoyin al’umma tare da tabbatar da cewa an ba su damar zaben abin da su ke so.