Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta Ta Kasa Inec, Ta Ce Ta Gano Na’urorin Tantance Masu Kada Kuri’a 21 Daga Cikin 69 Da Suka Bace A Lokacin Zaben Shugaban Kasa Da Na ‘Yan Majalisun Dokoki A Jihar Bayelsa.

Kwamishinan Zaben Jihar Monday Udo Tom, Ya Bayyana Haka A Wajen Taron Masu Ruwa Da Tsaki A Ofishin Hukumar Dake Yenagoa Babban Birnin Jihar.

Ya Ce A Wannan Karon Ba Za A Harhada Sakamakon Zabe A Ofishin Hukumar Dake Jihar Ba, Za A Yi Ne A Shelkwatan Hukumar, Inda Za A Fara Tun Daga Jami’an Gudanar Da Zaben A Rumfunan Kada Kuri’a.

Tom Ya Ce A Wannan Karon Hukumar Ta Gudanar Da Tsare-Tsare Da Za Su Taimaka Dan Ganin Ba A Samu Matsala Da Na’urar Tantance Masu Kada Kuri’ar Ba.