Kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar Sokoto Muhammad Sadiq, ya ce wasu mahara sun kashe mutane 16 a karamar hukumar Raba ta jihar Sokoto.

Sadiq ya bayyana wa manema labarai haka ne a daren Talatar da ta gabata, inda ya ce maharan sun afka wa kauyen Yawuri da ke karamar hukumar Raba da misalin karfe biyu na safiyar Talata tare da yin garkuwa da mutane shida a kauyen.

Wadanda aka yi garkuwa da su kuwa sun hada da wani Ayuba Tali, da Mamman Yawuri, da Musa Usman, da Kamusu Yawuri, da Atta Yawuri da Illiya Tali.

Ya ce bayan gari ya waye wasu ‘yan banga da ke kauyen su ka fantsama cikin dajin domin nemo mutanen da aka yi garkuwa da su, inda sakamakon barin-wuta a tsakanin su aka kashe mutane 16.

Sadiq ya ce mai yiwuwa burbushin maharan da su ka yin garkuwa da mutane ne a jihar Zamfara su ka yi hijira zuwa wasu bangarori na jihar Sokoto, ya na mai cewa duk da haka rundunar za ta yi kokarin ganin ta kamo wadannan mutane.
[cla��^0S��