Gwamna jihar Rivers Nyesom Wike, ya ce gwamnatin jihar sa ta nemi kotun hukunta manyan laifuffuka ta duniya ICC, ta tuhumi babban kwamandan rundunar sojin Nijeriya ta 6 Manjo Janar Jamil Sarhem.
Wike, ya ce kwamandan ya fito ya bayyana wa ‘yan Nijeriya dalilin da ya sa sojoji su ka afka wa jami’an hukumar zabe a yankin Ikwerre da Emohua da Okrika, wanda ake zargin satar kayan zabe ne da shirin fitar da sakamako.
Gwamnan ya kara da cewa, duk wani bayani da kwamandan zai yi ba zai sa a fasa gurfanar da shi ba.
Nyesom Wike ya kara da cewa, su na iyakar kokarin su tare da kotun duniya, kuma za su nema wa wadanda sojin su ka kashe su a wajen zaben hakkokin su.