Hukumar zabe mai zaman kan ta ta kasa INEC, ta mika wa shugaban kasa Muhammadu Buhari da abokin takarar sa Yemi Osinbajo shahadar lashe zaben da su ka yi.
An dai ba shugaba Buhari shahadar da ke nuna cewa shi ya zo na farko a zaben da aka yi a karshen makon da ya gabata.
Shugaba Muhammadu Buhari, ya mika godiya da duk mutanen da su ka zabe shi, tare da nuna jimamin sa ga wadanda su ka rasa iyalan su da ‘yan ‘uwa sakamakon rikicin da ya barke a lokacin zabe.
Buhari
ya bayyana haka ne, yayin jawabin da ya gabatar a wajen taron jam’iyyar APC da
ya gudana a Abuja, inda ya jinjina wa daukacin mutanen da su ka taimaka wajen ganin
ya sake zarcewa a kan mulki.
outbrae�^ဒ�