Wata babbar kotu da ke birnin Fatakwal na jihar Rivers, ta kori karar da aka shigar domin hana shugaba Muhammadu Buhari takara a shekara ta 2019 sakamakon rashin takardun makarantar shi.

Wani Lauya mai suna Lezina Amegua, ya roki kotu sa hukumar zabe ta hana shugaba Buhari takara, amma mai shari’a Ishaq Sani ya kori shari’ar sakamakon rashin sahihancin ta.

Alkalin kotun, ya ce bai ga yadda bayyana takardar shaidar makaranta ko madadin ta ya shafi ra’ayin shi a matsayin dan takara ba.

Kotun ta ce ba za ta lamunci yin amfani da ita wajen bata suna ko azarbabi da shishshigin wadanda ba su san kan abin da su ke kara a kai ba.

Amegua dai ya bukaci kotun ta ba shugaba Buhari umarnin ya bayyana takardar shaidar makarantar shi.