Jam’iyyar PDP, ta bukaci ‘yan Nijeriya su cigaba da kwantar da hankalin su, yayin da hukumar zabe ta bayyana shugaba Muhammadu Buari na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben da aka gudanar.

An dai bayyana shugaba Buhari a matsayin wanda ya yi nasara da kuri’u miliyan 15 da dubu 191 da 847, yayin da Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP ya samu kuri’u miliyan 11 da dubu 255 da 978.

Tsohon ministan sufuri Osita Chidoka, ya bukaci ‘yan Nijeriya su kwantar da hankalin su, ya na mai cewa jam’iyyar PDP ta yarda da kundin tsarin mulkin Nijeriya kuma ta na nan a kan tafarkin dimokradiya.

Tun farko dai Osita ya bukaci kada shugaban hukumar zabe Farfesa Mahmood Yakubu ya bayyana shugaba Buhari a matsayin wanda ya yi nasara.

Leave a Reply