Rundunar ‘yan sanda ta jahar Kano, ta kama wata mata mai suna Rashida Muhammad, bisa zargin hallaka mijin ta mai suna Adamu Ali a gidan su da ke rukunin gidaje na Dorayi a cikin garin Kano.
Rashida dai ta hallaka mijinna ta ne ta hanyar tunkudo shi daga gidan sama, inda sakamakon haka nan take ya ce ga garin ku nan.
Kakakin rundunar ‘yan sanda na jahar Kano DSP Abdullahi Haruna ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 8 na daren Litinin da ta gabata, amma sai a ranar Talatar da ta gabata ne su ka samu nasarar kama ta.
DSP Haruna, yace Rashida ta zargi mijin ta da yin waya da wata budurwar sa a cikin dakin su, inda ta yi kokarin kwace wayar domin tabbatar wa kan ta.
Ya ce ana cikin haka ne Rashida ta tunkudo mijin ta daga saman bene a haga yayi ta walagigi har sai dsaya tuntsuro kasa.
Kakakin ‘yan sandan ya cigaba da cewa, tuni an gudanar da jana’iza mamacin, ya na mai cewa za su gurfanar da Rashida gaban kuliya da zarar sun kammala bincike akan ta.