Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi jawabin godiyar sake samun nasarar zama shugaban Nijeriya karo na biyu, bayan sanarwar da hukumar zabe ta yi.
Buhari dai ya gode wa daukacin ‘yan Nijeriya, musamman Jigon jam’iyyar APC Bola Tinubu da Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Adams Oshimhole da kuma Rotimi Ameachi.
Shugaba Buhari, ya kuma gode wa dimbim jama’ar da su ka bada gudummawa a lokacin yakin neman zaben sa a fadin Nijeriya.
Ya ce duk da cewa an gudanar da zabe lafiya, an samu tashe-tsahen hankula a wasu wurare jifa-jifa, inda wasu batagari su ka tada fitintinu, ya na mai shan alwashin hukunta duk wanda ke da hannu wajen tada zaune tsaye a lokacin zabe.
A
karshe ya ja kunnen magoya bayan sa a fadin Nijeriya da cewa, kada murnar cin
zabe ta sa su rika tozarta ‘yan adawa.