Dakarun sojin Nijeriya sun yi kira ga shugaban kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau da sauran mayakan sa da su fito ayi gaba da gaba domin yin fadan karshe idan ba tsoro ba.

Wani jami’in Sojan Nijeriya ya bayyana haka a shafin sa na Instagram wanda ya ke amfani da shi wajen nuna ayyukan rundunar sojojin Nijeriya.

A cikin faifan bidiyon da sojan wallafa,  an ji wani soja ya na kira ga mayakan kungiyar Boko Haram su fito a buga tare da cewa, kungiyar Boko Haram ta fito a gwabza in da gaske ta ke.

Sojan ya cigaba da cewa sun dauka ‘ya Boko-Haram maza ne masu jini a jika da kuma da karfi, saboda haka su fito a fafata don kowa yasan matsayin sa.