Jam’iyyar PDP da dan takarar ta a kujerar shugaban kasa Atiku Abubakar sun shigar da kara kotu domin kalubalantar sakamakon zaben shugaban kasan da aka gunadar a ranar Asabar 23 ga watan Febrairu.
A ranar 19 ga watan Maris din nan ne Lauyoyin jam’iyyar PDP suka bayyana cewa, akwai hujjoji kimanin 50 cikin karar da suka shigar kotun zabe da ke Abuja, inda suke tuhumar hukumar zabe ta kasa INEC shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma jam’iyyar APC.
Idan dai ba a manata ba, a ranar 27 ga watan Febrairu ne hukumar INEC ta sanar da shugaban kasa Buhari a matsayin wanda ya yi nasara da kuri’u miliyan 15 da budu 191 da dadi 847 yayin da Atiku Abubakar ya samu kuri’u miliyan 11 da dubu 262da dari 978.
Sai dai daga cikin takardun karar da aka shigar kotun, jam’iyyar PDP ta ce daga cikin na’urar yanar gizon hukumar INEC, sakamakon gaskiya bayan an kammla tattaro dukkan kuri’un jihohi, Atiku Abubakar ya samu jimillar kuri’u miliyan 18 da dubu 356 da dari 732 yayin da shugaba Buhari ya samu kuri’u miliyan 16 da dubu 741 da dari 430.
Jam’iyyar
PDP ta kara da cewa, wannan shine sakamakon zaben jihohi 35 har da babban
birnin tarayya Abuja saboda ba a samu sakamakon zabe daga jihar Rivers ba har
zuwa ranar 25 ga watan Febrairu.