Al’umomin yakin Multafu da ke karamar hukumar Askira-Uba a jihar Borno, sun kawo kuka a kan hare-haren da Boko Haram ke ke kai masu.

Matanan yakin sun kuma yi matukar jimami a kan garkuwa da ‘ya’yan su mata biyu da ‘yan kungiyar  Boko Haram su ka yi.

Garin Multafu wai kauye ne da ‘yan kabilar Marghi ne masu sana’ar noma kuma ya yi iyaka da dajin Sambisa.

Idan dai ba a manta ba, a ranar 10 ga watan Maris din nan ne  ‘yan ta’addan sun kai hari a garin na Multafu tare da hallaka jami’in kato da gora da kuma jikkata al’umomin yakin da kona gidaje da kwashe kayan abinci.