Jami’an ‘yan sandan Nijeriya, sun saki tsohon shugaban hukumar zabe ta kasa Farfesa Maurice Iwu, wanda aka bada belin sa a jihar Imo.

Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Imo CP Dasuki Galadanchi, ya ce sun bada belin Maurice Iwu ne bayan ya shiga hannun su.

A kwana-kwanan nan ne hukumar yaki da cin hanci da rashawa ECC ta kama Farfesa Maurice Iwu, bayan ta samu izni daga hukumar ‘yan sanda.

Sai dai kwamishinan ‘yan sandan bai bayyana wa manema labarai abin da ya sa aka tsare Maurice Iwu ba.

Dasuki Galadanchi, ya ce tuni an bada belin Farfesan saboda ganin mutuncin sa da shekarun sa da kuma la’akari da irin gudumuwar da ya bada a Nijeriya.