Rahotanni na cewa, tuni dan takarar jam’iyyar PDP Atiku Abubakar ya fara shirin tara manyan Lauyoyin da za su tsaya masa a kotu domin kalubalantar sakamakon zaben shekara ta 2019.

Har yanzu dai jam’iyyar PDP ba ta yi na’am da sakamakon zaben shugaban kasa da hukumar zabe ta kasa ta bayyana ba.

Daga cikin Lauyoyin da ake sa ran Atiku Abubakar zai dauka akwai tsohon Ministan shari’a Kanu Agabi da Joe Gadzama da Chris Uche domin zuwa kotu.

Ana dai gab da kammala tattara sakamakon zaben ne, jam’iyyar PDP ta kira taron gaugawa bisa jagorancin Sanata Bukola Saraki a Abuja.

Jam’iyyar PDP ta nuna cewa an yi coge a zaben, inda ta nemi hukumar zabe ta dakatar da tattara sakamakon kuri’un domin akwai zaben jihohin da ba ta yarda da su ba.