Atiku Abubakar, Former Vice President, Presidential Candidate Of People’s Democratic Party, PDP
Atiku Abubakar, Former Vice President, Presidential Candidate Of People’s Democratic Party, PDP

Dan takarar shugaban kasa na jama’iyyar PDP Atiku Abubakar, ya yi watsi da sakamakon zaben shugaban kasa da hukumar zabe ta bayyana.

Hukumar zabe dai ta sanar da cewa, Shugaba Muhammadu Buhari na jam’iyyar APC ya samu kuri’u miliyan 15 da dubu 191 da 847, yayin da Atiku Abubakar ya samu kuri’u miliyan 11 da dubu 262 da 978.

Sai dai jim kadan bayan bayyana shugaba Buhari a matsayin wanda ya yi nasara, Atiku Abubakar ya fitar da sanarwar rashin amincewa da zakamakon zaben.

Atiku Abubakar, ya kuma kawo hujjojin da ya ke ganin cewa an tabka magudi a jawabin da ya fitar ranar Larabar nan, inda ya ce akwai tulin hijjoji na bidiyo, inda aka rika nuna yadda aka yi magudi a zaben da aka gudanar ranar Asabar da ta gabata.

Ya ce bai yarda da sakamakon zaben ba, kuma ya na kira ga magoya bayan sa cewa ba zai amince da sakamakon ba, ballantana har ya bada kai bori ya hau.