Kotun koli ta Nijeriya, ta tabbatar da hukuncin da wata babbar kotun tarayya da ke Legas ta zartar, na kwace kudi mallakin Patience Jonathan da yawan su ya kai dala miliyan takwas da dubu dari hudu.

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC, ta gano wasu makudan kudi a asusun bankuna daban-daban da Patience Jonathan ta boye.

A hukuncin da gamayyar alkalan kotun biyar su ka yanke, an yi watsi da daukaka karar da Patience Jonathan ta yi na hana gwamnatin tarayya kwace kudaden.

Kotun, ta kuma umurci Patience Jonathan ta bayyana a gaban babbar kotun tarayya, ta yi bayanin yadda ta samu kudaden.

Idan dai za a iya tunawa, wata kotu da ke zama a Abuja, ta ba jami’an gwamnati umurnin karbewa, tare da killace wasu gidajen Patience Jonathan, bisa zargin da ake yi mata na mallakar su ta hanyar da ba ta dace ba.