A’isha Buhari, Uwargidan Shugaban Kasa
A’isha Buhari, Uwargidan Shugaban Kasa

Uwargidan shugaban kasa A’isha Buhari, ta shawarci jam’iyyar APC da cewa idan an zo rabon mukamai a ba masu katin zama dan jam’iyyar kawai.

A’isha Buhari, ta bada shawarar ne a wajen wata liyafar cin abincin dare da aka gudanar a Daura, domin murnar nasarar da maigidan ta ya sake samu karo na biyu.

A makon da ya gabata ne, Shugaba Muhammadu ya kada Atiku Abubakar a zaben shugaban kasa da aka gudanar.

A’isha Buhari ta cigaba da cewa, kundin tsarin mulkin jam’iyyar APC ya bayyana cewa, masu katin jam’iyya kawai za a rika ba mukamai, don haka ya kamata jam’iyya ta girmama kundin tsarin ta yadda ya dace.