Wata majiya ta shaida wa manema labarai cewa, Shugaban kasa Muhammadu Buhari da shugabannin jam’iyyar APC, za su gana bayan zaben gwamnoni domin yanke shawara a kan tsarin rabe-raben mukaman majalisa ga yankuna.

Shugaba Buhari dai ya bayyana manufofin sa da cewa, a wannan karon ba zai zura ido ya na kallon yadda abubuwa ke gudana ba tare da ya tabuka komai ba.

Ya ce zai kasance a cikin duk wata tattaunawa da rikice-rikice a kan zaben manyan mukamai a majalissun tarayya.

A nata bangaren, jam’iyyar APC ta ce, ita ma za ta taka rawa  wajen zaben sabbin shugabannin majalisun tarayya.

Wasu daga cikin masu neman kujerar shugaban majalisar dattawa sun hada da sanata Ahmed Lawan, da Sanata Ali Ndume, da Sanata Danjuma Goje, da sanata Abdullahi Adamu, da sanata Ovie Omo-Agege.