Governor Aminu Waziri Tambuwal
Governor Aminu Waziri Tambuwal

Dan takarar kujerar gwamnan jihar Sokoto na Jam’iyyar PDP Aminu Waziri Tambuwal ya lashe zaben Gwmanan jihar karo na biyu.

Gwamna Aminu Waziri Tambuwal dai ya lashe zaben ne da tazarar kuri’u 341 kacal.

Yayin bayyana sakamakon, Shugabar hukumar zabe ta jihar Sokoto Fatima Mukhtar, ta ce Tambuwal ya samu kuri’u dubu 512,002, yayin da dan takarar jam’iyyar APC Ahmad Aliyu ya samu kuri’u dubu 511,661.

A ranar 9 ga watan Maris da ya gabata dai, Tambuwal ya na kan gaba ne da kuri’u dubu 489,558, yayin da Ahmad Aliyu na jam’iyyar APC ke da kuri’u dubu 486 da 145.

Sai dai a wancan lokacin, an bayyana zaben a matsayin wanda bai kammala ba, sakamakon soke kuri’u dubu 75 da 403 da aka kada a rumfunan zabe 136 da ke kananan hukumomin jihar Sokoto.