Dan takarar kujerar majalisar dattawa na Lawal Adamu Mr LA, Mazabar Kaduna Ta Tsakiya A Karkashin Jam’iyyar PDP
Dan takarar kujerar majalisar dattawa na Lawal Adamu Mr LA, Mazabar Kaduna Ta Tsakiya A Karkashin Jam’iyyar PDP

Dan takarar kujerar majalisar dattawa na mazabar Kaduna ta tsakiya a karkashin jam’iyyar PDP Lawal Adamu Mr La, ya samu izinin kotu na binciken kayayyakin zaben da aka yi amfani da su a babban zaben da ya gudana ranar 23 ga watan Fabrairu.

Idan dai za a iya tunawa, abokin karawar sa na jam’iyyar APC Uba Sani ne aka bayyana a matsayin wanda ya lashe zaben.

Sai dai Mr La ya garzaya Kotu, inda ya shigar da korafin kin amincewa da sakamakon zaben da ya kira mai cike da kura-kurai.

Tuni dai hukumar zabe ta amince da hukuncin kotun na ba Lawal Adamu Mr La damar binciken kayayyakin da aka yi amfani da su a zaben.