An bayyana tsohon ministan birnin tarayya Abuja Bala Mohammed na jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Bauchi da aka maimaita a ranar Asabar 23 ga watan Maris.

Hukumar zabe mai zaman kan ta ta kasa INEC dai ta bayyana sakamakon zaben ne bayan fuskantar tsaiko na tsawon kimanin sa’o’i 17.

Jami’in tattara sakamakon zaben Farfesa Kyari Mohammed bayyana sakamakon zaben a ranar Lahadin nan.

Farfesa Kyari ya ce, dan takarar jam’iyyar PDP Bala Mohammed ya samu kuri’u dubu 6 da 376, yayin da takwaran san a jam’iyyar APC kuma gwamna mai ci Abubakar Muhammad ke da kuri’u dubu 5 da 117.

Leave a Reply