Mataimakin shugaban rundunar ‘yan sandan Nijeriya DIG Anthony Ogbizi Micheal, ya bayyana kama wasu mutane 10 a da ake zargin su na cikin gugun ‘yan dabar da su ka tada hankulan jama’a yayin da ake kada kuri’a a mazabar Gama da ke karamar hukumar Nasarawa ta jihar Kano.

Yayin bayyana kamen, DIG Micheal ya musanta rahotannin da ke cewa akwai wadanda su ka rasa rayukan su sakamakon hargitsin da ‘yan dabar su ka haddasa, inda ya zargi marasa kishin kasa da yada labarun karya ta hanyar amfani da kafofin sada zumunta na zamani.

Rahotanni daga jihar Kano dai sun tabbatar da cewa, gungun ‘yan bangar siyasa dauke da makamai sun bayyana a mazabar Gama da ke karamar hukumar Nasarawa, inda su ka rika kai komo a kan babbar hanyar yankin.

‘Yan bangar, sun kuma hana jami’an sa ‘ido da manema labarai gudanar da aikin su a yankin, daga bisani kuma hargistin da ya tashi ya tilasta wa mutane da dama tserewa, ciki har da ‘yan jarida da su ka tsallake rijiya da baya.

Leave a Reply