Ahmad Abdurrahman, Kwamishina 'Yan Sanda Na Jihar Kaduna
Ahmad Abdurrahman, Kwamishina 'Yan Sanda Na Jihar Kaduna

Rundunar ‘yan sanda ta jihar Kaduna, ta sanar da kama wasu gaggan miyagun mutane 24, tare da kwace bindigogi takwas da alburusai da dama kamar yadda kwamishinan ‘yan sanda na jihar ya bayyana.

Kwamishina Ahmad Abdurrahman ya tabbatar da haka, yayin da yake ganawa da manema labarai a helkwatar su da ke Kaduna, inda ya ce sun samu nasarar ne bayan wani samamen musamman da su ka kaddamar a Kaduna.

Daga cikin wadanda aka kama, akwai mutane biyu da ake zargi da aikata laifin satar mutane tare da yin garkuwa da su, da masu laifin fashi da makami, da satar mota, da sayen kayan sata, da dabanci, da mallakar makamai ba bisa ka’ida ba.

Kwamishinan ya ce, sun kwace kananan bindigogi uku, da bindigar toka daya, da wasu bindigogi hudu da kuma alburusai da dama, sauran sun hada da motoci kirar Toyota guda 5, da na’urar komfuta guda 10, da allon Galaxy, da wayar Samsung, da atamfofi, da agogo, da adda da wata sherbebiyar wuka.

Kwamishinan ya ce, mutanen sun bada muhimman bayanai game da laifuffukan su ga jami’an ‘yansanda masu gudanar da bincike, kuma da zarar sun kammala zasu gurfanar da su a gaban kotu.