Akalla mutane biyu su ka rasa rayukan su, yayin da aka lalata motoci 35 tare da fashe-fashen shaguna a wani rikici da ya barke tsakanin bangarorin jam’iyyar APC a Oto-Awori da ke yankin Ijanikin a Legas.

Rikicin dai ya barke ne tsakanin magoya bayan dan takarar jam’iyyar APC daga bangaren Ojo, wanda ke neman kujerar majalisar jihar Legas, da wani abokin hamayyar sa da bai samu nasarar lashe zaben fidda gwani ba.

Wata majiya ta ce rikicin ya barke ne a lokacin da dan takarar APC mai suna Jafo ya ziyarci fadar Oloto na Awori, inda wasu matasa su ka yi kokarin hana shi shiga.

Leave a Reply