Jami’an tsaron sa kai na ‘yan kato da gora sun samu nasarar hallaka ‘yan bindaga 59 a wani gumurzu da suka yi a lokacin wani farmaki da ‘yan bindigar suka kai a jihar.
Daya daga cikin jami’an sa kan mai suna Bube Shehu, ya ce sun shafe fiye da sa’o’i 4 suna musayar wuta tsakanin su da ‘yan bindigar, wanda hakan ya yi sanadiyar mutuwar mutanan su 7.
Shehu ya ce a lokacin da su ke artabun da ;yan bindiyar a kauye Danjibga da ke jihar Zamfara sun samu dauki da jami’an sojin Nijeriya, lamarin da ya sa suka kashe ‘yan bindigar har su 59.
Garin na Danjibga da ke da nisan
kilomita 35 da garin Gusau, na fuskantar hare-haren ‘yan bindiga a lokuta
daban-daban, ba tare da samun taimakon jami’an tsaro ba.