Rundunar ‘yan sanda a jihar Kano ta ce ta yi nasarar kama wani mutum da wukake kimanin 6,750 a Kwanar Dumawa da ke hanyar zuwa jihar Katsina da kuma masu safarar miyagun kwayoyi.

Kwamishnan ‘yan sanda da aka kawo jihar Kano daga Katsina, M. I. Wakili, ya ce jami’an su sun kama mutumin da aka kama da wukake a kan hanyar sa ta shiga da su jihar Katsina, kuma kawo yanzu su na gudanar da bincike a kan lamarin kafin daukar mataki na gaba.

Haka kuma, kwamishinan ya ce jami’an ‘yan sandan sun yi nasarar kama wani mutum da madarar sukudai mai yawan gaske.

Wakili ya kara da cewa, sun kara kama wata motar dakon kaya da aka makare ta miyagun kwayoyi da aka shigo da su jihar Kano.

Kwamishinan ya ce ana sayar da irin wannan kwaya a jihar Kano kamar yadda ake sayar da goro, tamkar babu wata dokar hana tu’ammali da miyagun kwayoyi a jihar.

Ya ce Ko a cikin makon da ya gabata ma, sai da rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta kama ‘yan bangar siyasa 500 wanda ta ce zata  gurfanar da su a gaban kotu domin yi masu hukuncin da ya dace da laifin da su ka aikata.
GARGADI: IRAKI TA JA KUNNAN AMURKA