Hukumar kula da cutuka masu saurin yaduwa a Nijeriya NCDC ta sanar da karuwar mutane 37 da suka kamu da cutar zazzabin Lassa a fadin Nijeriya.

Babban jami’in hukumar Chikwe Ihekweazu ya kara da cewa, mutanen  sun kamu da cutar ne daga ranar 4 zuwa 10 ga watan Fabarairu.

Ihekweazu ya ce, a gwajin da suka gudanar a kan mutane 947 daga jihohi 20 da ake kyautata zaton su na dauke da cutar sun tabbatar da cutar a jikin mutane 324.

Jami’in ya kuna ce, tun bayan sake barkewar cutar a farkon shekarar nan ta 2019 akalla mutane 69 ta hallaka a jihohi 20 Nijeriya.

A karshe Chikwe Ihekweazu ya ce daga ranar 8 ga watan Fabrairu mutane 57 ne suka mutu sakamakon kamuwa da cutar, amma kawo yanzu adadin ya karu zuwa 69, matakin da ke nuna cewa cutar na ci-gaba da yaduwa a Nijeriya.

Leave a Reply