Fadar shugaban kasa ta bayyana cewa rade-radin da ake yi na cewa gwamnatin tarayya ta tsaida shirin Trader Moni ba gaskiya bane. Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo yayi wannan bayani ta bakin babban Hadimin sa.

A wani jawabi da Laolu Akande ya fitar a madadin ofishin mataimakin shugaban kasar, yace har gobe Trader Moni na aiki kuma an samu kananan ‘yan kasuwa har 30, 000 da aka rabawa jari bayan an kammala zaben Najeriya.

Mataimakin Shugaban kasa Osinbajo yace Trader Moni na nanSource: TwitterAkande yace an rabawa mutane da dama karin jari na N15000 domin su inganta kasuwancin su.

An zabi akalla mutane 30, 000 ne a kowace jiha har ma da Abuja. Yanzu haka dai kusan duk an ci ma wannan buri inji gwamnatin kasar.

Hadimin mataimakin shugaban kasar yace kusan mutane 30, 000 da aka rabawa wannan kudi bayan zabe wannan karo sun fito ne daga jihohohi 10.

Leave a Reply