Shugaban kungiyar sayar da kayan miya wanda yake kula da kasuwancin bangaren tattasai a babbar kasuwar sayar da kayan gwari wadda take cikin unguwar Mile 12 a jihar Legas Dauda Suleman Tarai, ya bayyana cewa noman kayan miya da manoman Arewa ke yi yana taimaka wa Najeriya da al’ummar cikin ta baki daya.

Dauda Sulaiman, ya yi wannan bayani ne a offishin sa da ke Mile 12 a lokacin da yake zantawa da wasu manyam manoman kayan miya daga Arewacin Nijeriya da suke kawowa Legas domin sayar wa al’umma.

Ya kara da cewa ya kamata gwamnatin tarayya da na sauran jihonin Arewacin Nijeriya a kokarin su na taima kama noman rani da na damina su kara kaimi a wajen bayar da tallafin noman kamar yan da suka sabayi a kowace shekara domin kara wa manoman kwarin gwiwa a wajen noman rani da na damina.

Ya ci gaba da yin kira gwamnatocin da su ci gaba da ba manoman tallafin takin zamani da kayan feshi na kwari da sauran kayaiyakin da manoman ke am fani da su a wajen noman ranin da na damina Sannan ya shawarci gwamnatocin da su bude kamfanonin da za a rika safarta kayan noman zuwa gwangwani domin manoman su rage asarar rubewar tattasai da tumatiri kamar yadda wadan su kasashen da suka ci gaba suke yi a kasashen su