Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta (INEC) ta mayar da martani a kan sanarwar da kasar Amurka ta fitar game da babban zaben 2019 da aka gudanar a Najeriya.

Amurka ta ce bata ji dadin yadda yawancin al’umma ba su fito zaben ba tare da amfani fiye da sojoji fiye da kima a yayin gudanar da zabukan.Wani sashi na cikin sakon da Amurka ta fitar ya ce:

A matsayin mu na tsaffin abokan huldar Najeriya, za mu cigaba sanya idanu a kan zaben da ake gudanarwa.

Ba mu da wata jam’iyyar ko dan takara da muke goyon baya.”Kamar yadda yawancin masu sanya idanu a zaben suka ruwaito, bamu ji dadin yadda al’umma basu fito sosai ba domin kada kuri’u da sayan kuri’u da rikici da kuma amfani da sojoji wurin cin zarafin mutane a wasu wurare.

“A yanzu da zaben ke zuwa karshe muna kira ga dukkan masu ruwa da tsaki su tabbatar an gudanar da sahihitar zabe kuma cikin zaman lafiya musamman a wuraren da za a yi zabe a ranar Asabar.

Sai dai a bangarensa, babban sakataren watsa labarai na INEC, Rotimi Oyekanmi ya ce an samu gagarumin nasara a zaben.

Leave a Reply