Asusun kula da kananan yara na duniya UNICEF ya ce sama da mutane miliyan uku da rabi ne ke bukatar tsabtacaccen ruwa a Nijeriya.
Asusun ya kara da cewa, wani jami’in ta da ke Nijeriya Muhammed Fall ya bayyana hakan a ranar juma’ar da ta gabata, a lokacin wani taron murnar ranar ruwa ta dunya.
Muhammad Fall ya kara da cewa, mutane sama da miliyan daya wadanda rikice-rikice ya raba su da gidajen su, wadanda da yawa daga cikin su suna fama da wannan matsalar ta rashin tsabtacaccen mahalli da wurin zama a halin yanzu.
Ya ce kusan mutane 800,000 ne ke cikin wannan hali, wanda kashi 79 cikin 100 yara ne da mata.
A Nijeriyan dai matsalar tsaro ta shafi mutane da dama musamman ma wadanda suke zaune a yankin arewa maso gabas, wanda hakan ya jawo musu zama a muhalli marar tsabta, da kuma yin amfani da gurbatacce ruwa.
A
shekarar 2017 sama da mutane dubu 5 ,ne suka kamu da cutar Amai da Gudawa, inda
mutane fiye da dubu 12 suka kamu da cutar a shekara ta 2018, daga cikin su mutane
175 ne suka rasa rayukan su.