Jami’an tsaro sun kama shugaban kamfanin yada labarai na AIT Raymond Dokpesi a filin sauka da tashin jiragen sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja, jim kadan bayan dawowar sa daga kasar Dubai domin duba lafiyar sa.
Kamfanin gidan Talabijin na AIT ne ya sanar da haka, inda ya ce daya daga cikin jami’an hukumar hana shige da fice ta kasa ya ce, umurni ne suka samu daga sama na cewa su kama shi da zarar ya dawo Nijeriya.
Idan dai ba a manta ba, Raymond Dokpesi dai na fuskantar tuhume-tuhume a kan zargin hadin baki da wasu wajen karkatar da kudaden da aka ware domin siyen makamai, wanda yawan kudaden suka kai naira biliyan biyu wanda ya amsa daga ofishin Sambo Dasuki.