Kotun sauraren korarraikin zabe da ke birnin Abuja ta ayyana dan takarar jam’iyyar adawa ta PDP, Ademola Adeleke a matsayin wanda ya lashe zaben jihar Osun bayan ta soke nasarar da Adegboyega Oyetola, na jam’iyyar APC ya samu a zaben da aka gudanar a watan Satumban 2018.
Tuni kotun ta umarci Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta, ta Najeriya INEC ta mika sabuwar takardar nasara ga Adeleke.
Wannan na zuwa ne bayan karar da Adeleke, ya shigar a gaban kotun, yana mai kalubalantar sakamakon da INEC ta fitar tare da zargin ta hada baki da jam’iyyar APC wajen sauya nasarar da ya samu.
Hukuncin kotun ya bayyana cewa, jam’iyyar PDP ta samu yawan kuri’un da ya kai dubu 254 da dari 698, in da APC ta samu kuri’u dubu 253 da dari 452.