Shugaban jam’iyyar APC Kwamared Adams Oshiomhole, ya nemi babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yi watsi da karar da aka shigar a kan sa.

Adams Oshiomhole ya maida martini ne, dangane da shari’ar da ake neman yi tsakanin sa da Bishof Osadolor Ochei, wanda ya zargi Oshiomhole da aikata ba daidai ba a lokacin ya na gwamnan jihar Edo.

Lauyan Oshiomole Terhemba Gbashima ya shaida wa kotun cewa, karar da Osadolor Ochei ya shigar ba ta da matsaya a shari’a, domin an shigar da ita ne watanni 18 bayan zargin aikata laifin.

Gbashima, ya ce ya kamata a ce an maka tsohon gwamnan zuwa Kotu a lokacin da ake zargin sa da aikata laifi, don haka Lauyan ya roki Alkalin kotun ya yi watsi da karar.

Lauyar mai kara Uju Chukwurah, ta nemi Alkali Anwuli Chikere ya cigaba da bincike, ta na mai nuna cewa abin da Lauyan wanda ake tuhuma ya ke dogoro da shi na a yi watsi da karar ba gaskiya ba ne.

Leave a Reply