Rahotanni sun bayyana cewa, akalla mutane 30 ne su ka rasa rayukan su a wani hari da wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne su ka kai a garin kwari da ke karamar hukumar Shinkafi ta jihar Zamfara.
Dakta Suleiman Shu’aibu Shinkafi ya shaida wa manema labarai cewa, lamarin ya faru ne a ranar kasuwar Shinkafi, a daidai lokacin da jami’an sa-kai su ke kokarin raka jama’a domin cin kasuwa.
Ya ce a ranar kasuwar, barayin sun bude wa jami’an sa-kai da kuma ‘yan kasuwar wuta su ka kashe su gaba daya.
Dakta Shinkafi ya kuma koka bisa rashin tsaron da su ke fama da shi a yankin na Shinkafi, inda ya ce akwai karancin sojoji da jami’an ‘yan sanda.