Rahotannin na nuni da cewa, kwamitin zartarwa na jam’iyyar APC na kasa ya dakatar da gwamnan jihar Ogun Ibikunle Amosun da takwaran sa na jihar Imo Rochas Okorocha daga jam’iyyar.

Wata majiya ta ce, kwamitin ya gabatar da wata bukata ga kwamitin zartarwa na jam’iyyar, domin duba yiyuwar korar gwamnonin biyu daga jam’iyyar gaba daya.

Kwamitin dai ya dauki matakin ne, a wajen wani taro da ya gudanar a Abuja, inda ya ce sun yanke hukuncin ne, biyo bayan yi wa jam’iyyar zagon kasa da gwamnonin su ke yi.

An dai zabi Amosun da Okorocha zuwa majalisar dattawa a karkashin jam’iyyar APC, amma su na goyon bayan ‘yan takarar gwamnonin jihohin su na wasu jam’iyyu daban a zaben gwamnoni da za a gudanar ranar 9 ga watan Maris.