Dan takarar gwamnan jihar Kaduna na jam’iyyar APGA Dakta Polycaro Gankon, da takwaran sa na jam’iyyar LM Kwamred Ezekiel Habila, sun janye wa dan takarar jam’iyyar PDP Isa Ashiru Kudan.
Da ya ke zantawa da manema labarai a madadin takwaran sa na jam’iyyar LM, Dakta Gankon ya ce sun yanke shawarar janye wa ne, bayan tuntubar ‘yan jam’iyya da ‘yan’uwa da abokai domin su hada karfi su ceto jihar Kaduna daga kalubalen da ta ke fuskanta.
Ya ce ba su fuskanci matsin lamba a kan su janye takarar sub a, kuma ba su janye saboda an ba su kudi ba.
Dakta Gankon ya cigaba da cewa, sun yanke shawarar ne domin kishin jihar Kaduna, kuma su na kira ga dukkan magoya bayan su, su mara wa jam’iyyar PDP baya a zaben gwamna domin ta kawo masu ci-gaba.
Ya ce su na kira ga magoya bayan su da cewa, kada su bari sakamakon zaben shugaban kasa da aka yi magudi ya karya ma su gwiwa, dole mu tashi tsaye wajen ganin snu yi tururuwar fita su zabi jam’iyyar PDP.