Kungiyar Boko Haram ta hana Gwamnan Jihar Yobe Ibrahim Gaidam kada kuri’ar sa a zaben shugaban kasa da ya gudana a ranar Asabar.

A cikin wata sanarwa da ofishin jami’in hulda da jama’a gwamnan ya fitar, ta ce Gwamnan ya yanke shawarar janyewa daga kada kuri’ar sa ne sakamakon hare-haren da kungiyar ta kaddamar a wasu wurare biyu a jihar.

Sanarwar ta kara da cewa, Gwamnan ya gaza zuwa mazabar sa ta Bukarti da ke kusa da garin Gaidam da kimanin kusan kilomita 230 daga babban birnin Jihar.

Rahotanni sun ce, hankula sun kwanta a halin yanzu, yayin da tuni aka fara fitar da sakamakon zabe a na wasu wurare daban daban da ke fadin Nijeriya.