Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano CP Muhammad Wakili ya ce ba zai bari a hada kai da shi wajen aikata duk wani Ma-sha-Ah ba.
Wakili ya bayyana haka ne a wata zantawa da ya yi da manema labarai, ya kara da cewa babu wanda ya ke tsoro a duniya sai mahaliccin sa, don haka babu wata baraza da wani zai yi masa.
Kwamishinan ya kuma yi nuni da cewa, ya na tsoron haduwa da Mala’ikun kabari, saboda haka babu wanda zai sa shi ya aikata abunda bai dace ba a bakin aikin sa.
Wakili
ya zama kwamishinan jihar Kano ne ana daf da fara zaben 2019, don haka ya ke
kira ga daukacin al’umma cewa, ba za a hada baki da shi domin ayi rashin
gaskiya ba.