Rundunar Sojojin Nijeriya ta sanar da rasuwar wani soja mai mukamin laftanant da aka kashe a rikicin jihar Rivers.
jaridar Premium Times ta ruwaito cewa, a kalla mutane hudu ne suka rasa rayyukan su a rikicin da ya barke a jihar.
Sanarwar mutuwar sojan dai, ya fito ne daga bakin sabon kakakin rundunar sojojin Nijeriya kanar Sagir Musa.
Kanar Musa ya ce, mutane bakwai ne suka mutu ciki har da soja, sakamakon hari da wasu mutane suka kai musu lokacin da su ke sintiri.
Rahotanni daga hedkwatan sojin Nijeriya ta ce an kaima dakarun sojin rundunar 6 harin ne a lokacin da su ke aikin sintiri domin kare lafiya da dukiyoyin al’umma a karamar hukumar Akuku Toro da ke jihar Rivers.
Maharan dai sun kaiharin kwantar baune ne a wani babban titi inda suka bude wa sojojin wuta a yayin da suke kokarin wucewa, wanda hakan ya yi sanadiyar mutuwar mutane 6 daga cikin maharani, amma laftanant guda na soja ya mutu a lokacin musayar wutar.