Rahotanni daga jihar Kano na cewa, an tsinci gawar dan kasar Lebanon da wasu ‘yan bindiga su ka sace a bakin aikin sa ranar Talatar da ta gabata.

Wata majiya ta ce, an tsinci gawar mutumin ne a kan hanyar Maiduguri a ranar Alhamis da ta gabata.

Idan dai za a iya tunawa, wasu mutane hudu ne sun sace wani kwararren injiniya dan kasar waje da ke aiki a Kano.

Mai magana da yawun Rundunar ‘yan Sanda ta jihar Kano Abdullahi Haruna, ya ce babu shakka lamarin ya faru, kuma tuni an soma bincike domin gano bakin zaren.