Jam’iyyar PDP a jihar Benue, ta nada Sanata Dino Melaye da Gwamna Samuel Ortom a matsayin wakilan zabe da za su yi aiki a zaben gwamna da za a maimaita a jihar.

Haka kuma, jam’iyyar ta zabi tsohon shugaban majalisar dattawa David Mark da tsohon gwamnan jihar Gabriel Suswan da tsohon Ministan cikin gida Abba Moro a matsayin wakilan zaben da za a gudanar kamar yadda rahotanni su ka bayyana.

Wata majiya ta ce, an mika sunayen mutanen a cikin jerin sunayen wakilai 24 da PDP ta mika wa ofishin Hukumar Zabe a matsayin wakilan su na zaben.

A wani bangare kuma, hukumar zabe ta kasa ta ce, babu wata kotu da ke da ikon hana ta maimaita zabe a jihar Adamawa a wuraren da zaben bai kammala.

Kwamishinan zabe na jihar Adamawa Barista Kassim Gaidam, ya ce doka ba ta ba kotu ikon hana hukumar zabe gudanar da ayyukan ta ba kamar yadda wasu rahotanni su ka ruwaito ba.