Bayanai daga rahoton kudi da ayyuka na kamfanin man fetur na kasa NNPC ya nuna cewa, an fasa bututun mai 257 mallakar kamfanin a cikin watan Disamba na shekara ta 2018.
Hakan ya sa an samu hauhawa daga bututu 60 da aka fasa daga watan Nuwamba da kusan 197.
Adadin barnar da aka samu a watan Disamba ya fi na bututun mai 219 da aka shigo da su daga watan Oktoba na shekara ta 2018, sannan daga cikin bututu 257, daya ya ki gyaruwa yayin da shida su ka tsatstsage.
A wani rahoton da aka wallafa a shafin yanar gizo na kamfanin, bututun mai shida sun gaza gyaruwa, sannan biyu sun tsatstsage daga cikin 197 da aka lalata a watan Nuwamba.
Tashoshin da aka fi samun yawan fashe-fashen dai sun hada da na Ibadan zuwa Ilorin 90, da Mosimi zuwa Ibadan 69, da kuma Atlas Cove zuwa Mosimi network 57.