Ana ci-gaba da kai ruwa rana a kan zaben jihar Rivers, bayan wata babbar kotu da ke Abuja ta dakatar da ci-gaba da tattara sakamakon zaben jihar.
Dakatarwar dai ta zo ne, bayan karar da dan takarar gwamna na jam’iyyar AAC a jihar ya shigar.
Jam’iyyun Labour Party da APDA su ma sun kai hukumar zabe kara a babbar kotun tarayya da ke Abuja.
Jam’iyyar AAC ta bukaci kotu ta dakatar da huklumar zabe daga tattara ko kuma bayyana sakamakon zaben da ta dakatar a jihar Riveres.
Kotun ta bukaci hukumar zabe ta bayyana gabanta ranar Juma’a domin fara sauraren karar da jam’iyyar AAC da dan takarar ta su ka shigar a kan zaben.
Idan dai za a iya tunawa, a ranar Talatar da ta gabata ne, babbar kotun tarayya da ke Abuja ta dakatar da tattara sakamakon zaben jihar Bauchi.