Gwamna Aminu Bello Masari na Jihar Katsina, ya ce ya na ganawa da Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo da shugabannin hukumomin tsaro, dangane da yawaitar hare-hare da garkuwa da mutane da su ka addabi jihar Katsina.

Masari ya bayyana haka ne, a lokacin da ya ke amsa tambayoyin manema labarai a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja, inda ya ce daga cikin dalilan ziyarar har da taya Osinbajo murnar lashe zaben shekara ta 2019 da APC ta yi.

Ya ce kafin ya bar Abuja zai gana da shugaban rundunar ‘yan Sandan Nijeriya da Babban Daraktan hukumar tsaro ta farin kaya DSS.

Masari ya cigaba da cewa, ya na so su kara tattauna matakan tsaron da za a kara dauka domin kara karfafa tsaron da a yanzu jami’an sojoji ke yi da wanda sauran wadanda abin ya shafa ke badawa.