Abdul-Aziz Yari, Former Governor Of Zamfara Sate
Abdul-Aziz Yari, Former Governor Of Zamfara Sate

Gwamnan jihar Zamfara Abdul-Aziz Yari, ya ziyarci fadar shugaban kasa domin ganawa da shugaba Muhammadu Buhari a kan matsalar tsaro da ta addabi jihar Zamfara.

Jim kadan bayan ganawar, gwamna Yari ya shaida wa manema labarai cewa, ya kai wa Buhari korafi ne a kan yadda ‘yan bindiga ke ci-gaba da addabar al’ummar sa.

Abdul-Aziz Yari, ya ce babu sauran maganar sulhu tsakanin gwamnati da ‘yan bindiga a jihar Zamfara, domin sau uku ya na neman sulhu da su, amma hakan bai haihar da da mai ido ba.

Ya ce a zaman su na farko sun gayyaci Sojoji, da jami’an tsaro na DSS, da ‘Yansanda, da wasu Sarakunan gargajiya, kuma sun ga irin makaman da su ke amfani da su, wadanda hatta jami’an tsaron da ke Zamfara ba su da irin su.

Gwamnan ya cigaba da cewa, a wuri daya kacal sun samu bindigogi samfurin AK 47 sama da 500, yayin da a jihar Zamfara ba su da guda 90, don haka da su ka yi masu tayin sulhu amma su ka ki amincewa.