Wasu da ake zargin ‘yan daba ne, sun kona ofishin hukumar zabe mai zaman kan ta ta kasa a karamar hukumar Ibesikpo Asuntan da ke jihar Akwa-Ibom.

Lamarin dai ya afku ne a ranar Juma’ar nan, wanda ya yi sanadiyar lalacewar wasu kayayyakin zabe.

Jihar Akwa-Ibom ta na daga cikin jihohin da aka samu yawan rikice-rikice a lokacin zaben Shugaban kasa da na majalisun dokoki na tarayya.

Kwamishinan zabe na jihar Mike Igini ya ziyarci wurin da lamarin ya faru, sai dai babu wani bayani da ke nuna lamarin zai shafi zaben ranar Asabar, 9 ga watan Maris a yankin.