A yayin da aka gudanar zaben gwamnoni a jihohi 29 a Najeriya, wani al’amari da ke ba mutane da dama mamaki shi ne batun yadda ake sayen kuri’u da kudi ko kayan masarufi ya zama ruwan dare.

Sayan kuri’un mutane dai a lokacin zabe babban laifi ne a dokar Najeriya.

A ranar Juma’a ce aka ce an ga yadda ake rabon kayayyaki da nufin sayan kuri’u a Jihohin Kwara da Legas.

Haka zalika a ranar Asabar da ake gudanar da zaben, an ga yadda jam’iyyu ke rabawa mutane naira 200 ko 100 a wasu yankunan don su zabe su.

Hukumar EFCC ma ta wallafa a shafinta na Twitter cewa ta kama wasu makudan kudade da take zargin za a yi sayen kuri’u ne da su a jihar Benue.

A kokarin ta na kama wadanda ke dauke da kudin ne ma, wasu ‘yan daba suka kai wa jami’an hukumar hari tare da lalata motar bas da EFCCn ke sintiri da ita.