‘Yan bangar siyasa sun tsorata masu zabe a wasu mazabun da ke Lokoja babban birnin jijar Kogi.

Wani da abin yafaru a kan idon sa Sunday Adwjoh, ya tabbatar wa kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN cewa wasu mutane da dama daga mazabar Karaworo sun tsere sun bar mazabun su.

Adwjoh, wanda aka tattauna da shi ta wayar tarho ya ce suna kan layin zabe kawai sai suka ji harbin bindiga inda suka waste domin ceton ran su.

Hakazalika a mazabar Oke Egbe ta Yagba ta yamma rahotanni sun bayyana cewa an harbi wani mutum a kafar sa lokacin da wasu mutane suka kai mamaya mazabar don sace akwatin zabe da sauran kayayyaki.

Leave a Reply